An sake damke akalla mutum 551 daga cikin fursunoni 879 da suka tsere sakamakon harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje da k Babban Birnin Tarayya Abuja a Talatar da ta gabata.
Ya zuwa hada wannan labari, akwai ragowar fursunoni 328 da ake nema ruwa a jallo don a sake damke su.
- Buhari ya kai ziyara gidan yarin Kuje kafin ya wuce Senegal
- ‘Abba Kyari bai tsere daga gidan yarin Kuje ba’
Yayin harin, wasu mutum hudu daka cikin fursunonin da kuma jami’in NSCDC daya suka rasa ransu, yayin da mutum 16 suka ji rauni ana kuma ci gaba da yi musu magani.
Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa ta ce, ana ci gaba da kokarin ganin an sake kamo ragowar fursunonin da suka tsere baki daya.