’Yan Sanda a Jihar Oyo sun sake cafke wani matashi da ya yi kaurin suna wajen kashe mutane mai suna Sunday Sodipe.
An cafke matashin mai kimanin shekaru 19 ne mako biyu bayan ya tsere daga hannun ’yan sandan a unguwar Akinyele da ke Ibadan, babban birnin jihar.
A ranar 11 ga watan Agusta, Sunday ya kufce daga hannun ’yan sandan bayan kama shi ranar 17 ga watan Yuli, ya kuma amince da kisan mutane shida, ciki har da wata mai juna biyu
Kakakin Rundunar, SP Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da hakan, sai dai bai yi cikakken bayani kan yadda aka kama wanda ake zargin da wurin da aka ajiye shi yanzu ba.
Idan dai za a iya tunawa, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin kara tsananta bincike don ganin a cafke matashin.
Rundunar ’yan sandan ta sanya tukwicin Naira dubu 500 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama Sunday din.
An dai zargi mutumin da shirya hare-haren da suuka yi sanadiyyar mutuwar mutane babu gaira babu dalili a Akinyele, kafin ya tsere daga hannun ’yan sandan.