Wasu da ake zargin barayi ne a ranar Laraba sun sace wayar tsohon Ministan Watsa Labarai, Labaran Maku a kotun daukaka kara da ke Abuja.
Ana zargin an sace wayar ne yayin zaman kotun, jim kadan bayan ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Nasarawa.
- Mata ta nemi kotu ta nema wa ɗanta uba daga cikin mazajenta biyu
- APC Na Kokarin Mayar Da Najeriya Siyasar Jam’iyya Daya —Atiku
Kotun dai ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ke sauraron karar da Gwamnan Jihar, Abdullahi Sule, ya shigar, yana kalubalantar nasarar da kotun sauraron kararrakin zabe ta ba dan takarar PDP, David Umbugadu.
Labaran Maku dai na ɗaya daga cikin kusoshin jam’iyyar PDP da suka rufa wa Umbugadu baya yayin zaman kotun.
Sai dai bayan an kammala zaman kotun, an ga Labaran Maku ya koma gefe yana tambayar ko akwai wanda ya ga wayar tashi.
Amma duk kokarin da hadimai da magoya bayansa suka yi na neman wayar a harabar kotun, ya ci tura.