✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace Shugaban APC na Jihar Nasarawa

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Mista Philip Tataru Shekwo. Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Bola Longe ya tabbatar da…

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Mista Philip Tataru Shekwo.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “‘yan bindiga masu yawa da ba a gano daga inda suka fito ba, sun shiga gidan Shugaban APC na Jihar Nassarawa a garin Lafia, ranar Asabar da misalin karfe 11 na dare, suka yi awon gaba da shi, babu wanda ya san inda suka kai shi.”

Mista Bola Longe ya ce an zuba jami’an tsaro a cikin dazukan jihar don ganin an  kubutar da Mista Shekwo daga masu garkuwar.

Mazauna yankin Bukan Sidi da ke kwaryar garin Lafiya sun ce maharan sun yi ta harbi a sama don kada su samu kalubale daga jami’an tsaro da ke makwabtaka da wurin.