A yanzu haka Majalisar Dattawa na cikin rudu da rashin tabbas na yadda aka sace sandar majalisar.
Ita dai wannan sandar, wadda ita ce ke gaba da komai a majalisar, wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka shigo suka sace ta a safiyar yau.
Mutanen wadanda za su kai biyar, sun shigo majalisar ne a lokacin da mataimakin shugaban majalisar, sanata Ike Ekweremadu ke jagorantar zama, sannan suka dauki sandar suka yi awon gaba da ita sannan suna fitowa suka shiga mota kirar jeep suke tsere.
Ita dai wannan sanda, kusan idan babu ita, shi ke nan babu zama domin kuwa zai yi wuya a gabatar da wani kuduri ko doka ba tare da sandar ba.