✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace mahaifiyar Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan Kogi

An dai sace ta ne jim kadan bayan ta idar da sallar Isha.

’Yan bindiga sun sace mahaifiyar Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan Kogi, Abdulkarim Jamiu Asuku, Hajiya Seriya Raji.

Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa gidanta da ke Karamar Hukumar Adavi a Jihar kawanya ne da daren ranar Litinin.

Wani ganau ya shaida cewa an saceta ne jim kadan bayan ta idar da sallar Isha a masallacin da ke cikin gidanta, wanda ke rukunin gidaje na Inese/Ovakere da ke Karamar Hukumar.

A cewar majiyar, maharan, wadanda yawansu ya kai kusan 16 sun yi amfani da kyallaye wajen rufe fuskarsu don kada a gane su.

Majiyar ta kuma ce sun shiga gidan ne ta kofar masallacin kafin su yi awon gaba da ita zuwa wani waje da ba a san ko ina ne ba.

Sai dai har zuwa yanzu ba su tuntubi iyalanta ba don tattauna batun kudin fansa.

Harin dai na zuwa ne ’yan makonni kadan bayan Kwamishinan Muhalli na Jihar, Adewale Omofaiye ya tsallake rijiya da baya daga hannun masu garkuwar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, kakakin ’yan sandan Jihar, William Aya bai amsa kiran wayar da rubutaccen sakon da wakilinmu ya tura masa ba a kan lamarin.