✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace magunguna masu hadari a ma’adanar NAFDAC

An gargaji mutanen da suka sace kaya a rumbun Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), da ke Narayi, Jihar Kaduna da cewa akwai…

An gargaji mutanen da suka sace kaya a rumbun Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), da ke Narayi, Jihar Kaduna da cewa akwai magunguna da suka lalace da masu lahani a cikin kayan.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi gargadi tare da cewa duk wanda ya sha maganin zai iya kamuwa da rashin lafiya ko ma ya mutu.

Ta kara da cewa kamfanin sarrafa abinci da ke Kakuri da aka saci hatsi ya sanar da ita cewar hatsin na dauke da sinadari mai lahani ga dan Adam.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwa, ya bukaci mazauna su saka ido tare da tantance abinci ko maganin da za su saya domin kauce wa sayen masu lahani.

“Gwamnatin Jihar Kaduna na kira ga mutane da su taimaka wajen tona asirin duk wanda suka sani yana da hannu a satar kayan”, inji Aruwan.

A ranar Asabar mutane sun yi ta fasa rumbunan gwamnati suna kwasar kayan tallafin COVID-19, kafin daga baya su shiga satar kayan jama’a  da suka hada da na abinci, kujeru da kuma laturoni.

Hakan ya sa gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Kudu, kafin daga baya dokar ta zama game gari, domin dakile karya doka da oda.