Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi karin haske kan satar da aka yi a gidansa da ke yankin Gwarimpa, Abuja, inda ya ce waxanda ake zargin sun sace duk wani abu da za a iya xauka a gidan. Jonathan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Kakakinsa Ikechukwu Eze ya fitar a ranar Talata, bayan da manema labarai da sauran jama’a suka nemi hakan daga gare shi. Ya ce “An gano satar ce a watan jiya, inda aka kai rahoto ga hukumomin da suka kamata. Kuma nan take ’yan sanda suka fara bincike inda suka kama tare da tsare waxansu daga cikin waxanda ake zargin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.” Idan za a iya tunawa hukumomin ’yan sanda sun tsare waxansu ’yan sanda uku, kan zarginsu da hannu a satar ta tsohon gidan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan na Gwarimpa.
Bayanai sun ce, ’yan sandan za su gurfana gaban kotun ’yan sanda, inda ake sa ran za a kore su daga aiki kai laifin sata.
Wata majiya da take da masaniya kan binciken da ake yi a kan batun, ta ce ’yan sandan waxanda suke gadin gidan sun yi ikirarin sayar da wasu daga cikin kayayyakin da ake zargin an sace daga gidan.
Majiyar ta ce kayayyakin da ake zargin ’yan sandan da sacewa sun haxa da kujeru da kayan kawar xaki masu tsada da jerin akwatunan talabijin da na’urorin sanyaya xaki da malafofi da suturu irin na Turawa da na kabilar Ijaw.
Bayanai sun ce an kusan kammala yadda za a kori jami’an daga aiki kan aikata rashin xa’a.
“Bincike kan satar ya yi kusan kammala, kuma tabbas ne ’yan sandan da suke da hannu a lamarin za su rasa aiki saboda nuna rashin xa’a. Ta yaya za su sace abin da aka tura su su tsare?” majiyar ta bayyana.
Rundunar ’Yan sandan Birnin Tarayya, ta faxi a wata sanarwa cewa ta fara bincike a kan lamarin, inda ta ce binciken farko ya nuna an gano wasu kayayyaki “sun bace a gidan.”
Kakakin Rundunar Ajunguri Mamzah ya ce, “An kama ’yan sandan da suke aikin tsaro a gidan ana yi musu tambayoyi. Kuma ana bincike domin gano hakikanin abin da ya faru,” inji Anjuguri Manzah.