Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace dan majalisar dokokin jihar Kaduna Suleiman Ibrahim Dabo mai wakiltar Zariya akan hanyar Kaduna zuwa Zariya. Lamarin ya auku ne a yau Juma’a nan bayan anga motar sa kirar Toyota Camry mai lamba No ZAR 972 TL a kusa da kauyan Farakwai akan titin.
Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni an aika ma’aikata zuwa garin domin yin binciken lamarin.
Ya kuma bayanna cewa, an tsince karin shaidar aiki a cikin motar mai dauke da sunansa. Ya ce, tuni sun aika da jami’an su domin gano inda yake.