✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An sace daliban Islamiyya 200 a Neja

Tun da safe ’yan bindigar ke aikata ta’asa daban daban a garin.

Kimanin daliban Islamiyya 200 rahotanni suka bayyana an sace a garin Tegina na Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja da maraicen ranar Lahadi.

Sace daliban ya biyo bayan harin da ’yan bindigar suka kai a garin na Tegina tun da farko a ranar Lahadin inda maharan suka yi ta harbi kan mai tsautsayi.

Wasu rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba da ke fitowa daga garin sun ce babu tabbas kan adadin daliban da aka sace, sai dai an yi awon gaba da dama. 

Bayanai daga garin sun tabbatar da ’yan bindigar sun shiga garin tun da safiyar Lahadin inda suka yi ta aikata ta’asa daban daban. 

Sai dai neman jin ta bakin Kakakin rundunar yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ci tura a yayin tattara wannan rahoton.