Mutum daya aka harbe murus sai kuma dalibai da malamai da aka yi awon gaba da su yayin da masu garkuwa da mutane suka auka wa Kwalejin Nuhu Bamalli da ke garin Zariya a Jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Alhamis da daddare kamar yadda Jami’in Hulda da Al’umma na Makarantar, Abdullahi Shehu ya shaida wa Aminiya.
Wasu rahotanni na cewa, dalibin da ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga ya mutu ne a kan hanyar zuwa Asibiti.
Daga cikin malaman da aka sace akwai Mista Habila Nasai da kuma Mista Adamu Shehu.
Wannan shi ne hari na uku mafi girma da aka kai manyan makarantu a Jihar Kaduna cikin watanni ukun da suka shude.
A ranar 11 ga watan Maris na 2021 ne ’yan bindiga suka yashe dalibai a Kwalejin Harkokin Noma da Gandun Daji ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Afaka a Karamar Hukumar Igabin Kaduna.
Haka kuma, a ranar 20 ga watan Afrilun 2021 ne aka yi garkuwa da daliban Jami’ar Greenfield da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar.
Wannan sabon hari na baya bayan nan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe duk wasu masu tayar da zaune tsaye a kasar.
Cikin wata hira da ya yi da safiyar ranar Alhamis da Gidan Talibin na Arise, Shugaban ya ce al’ummar kasar su zuba idanu tare da kasancewa cikin tsammani na inganta harkokin tsaro a kasar.
Sai dai duk ire-ren wannan alkawura da masu rikda madafan iko a kasar ke ci gaba da yi, matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a fadin kasar.