Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta sanar da ranar hudu ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar da za a sake bude makarantu a jihar.
Kwamishinan Watsa Labaran na jihar, Mista Ini Ememobong, ya sanar da hakan ranar Alhamis a Uyo, babban birnin jihar a taron masu ruwa da tsaki na jihar.
- Coronavirus ta kashe Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Akwa Ibom
- An kama mai dafa abinci da ruwan wankan gawa a Akwa Ibom
- An cafke ‘yan kungiyar asiri 54 a Akwa Ibom
Ya ce gwamnatin ta shirya hakan ne saboda gudun lalacewar jadawalin karatun yara, inda ya ce zangon karatu na farko zai kare ne ranar 23 ga Janairun 2021.
Ya ce gwamnan jihar ya umarci kwamishinan Ilimi na jihar, da ya tabbatar da kowacce makaranta ta kiyaye matakan kariya daga cutar COVID-19.
Har ila yau, kwamishinan ya ce gwamnatin za ta ci gaba da ginin katangar makarantu a jihar, don bunkasa makarantu a jihar.
Mista Ini ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar za ta samar mazubin ruwa domin wanke hannu ga dalibai a makarantun jihar.
Daga nan sai ya bukaci Kwamishinan Lafiya na jihar da ya ci gaba da wayar da kan jama’ar game da irin illar da cutar ke da ita ga al’umma.