✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa Chelsea a kasuwa saboda rikicin Rasha da Ukraine

Abramovich ya amince zai shiga sulhu tsakanin Rasha da Ukraine.

Mai kungiyar Chelsea kuma hamshakin attajirin nan dan kasar Rasha, Roman Abramovich ya sanya kungiyar a kasuwa a sakamakon ci gaba da fuskantar matsin lamba na takunkumi daga gwamnatin Birtaniya kan alakarsa da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin.

Rahotanni sun ce Abramovich na neman siyar da Chelsea da wuri wanda hakan mataki ne da ya dace ya kuma yanke shawara mai kyau a wannan halin da ake ciki biyo bayan mamayar da dakarun sojin Rasha suka yi wa Ukraine.

An dai zargin Abramovic yana da alaka da kut-da-kut da birnin Moscow da kuma Shugaba Vladmir Putin wanda kwanaki bakwai da suka gabata ya bai wa dakarun sojin kasarsa umarnin mamaye Ukraine.

Bayanai sun Chelsea na iya fuskantar koma baya ta fuskar kasuwanci da ta kwallon kafa saboda Abramovic da Rasha wanda a dalilin haka yake son sayar da ita cikin gaggawa domin gudun abin da ka iya zuwa ya komo.

A baya dai Abramovich ya bayyana cewa ba shi da niyyar sayar da kungiyar inda ya mika ragamar gudanarwarta a hannun kwamitin amintattu na kungiyar, amma a sakamakon yadda rikici ke kara kamari tsakanin Rasha da Ukraine da kuma kiraye-kirayen neman gwamnatin Birtaniya ta kara tsananta takunkumi a kansa babu makawa ya sanya kungiyar a kasuwa.

Wani attajiri dan kasan Switzerland mai shekaru 86, Hansjorg Wyss ya bayyana cewa an tuntubi game da batun sanya kungiyar a kasuwa, inda jaridar wasanni ta 90min ta ruwaito cewa wani attajirin Birtaniya, Sir Jim Ratcliffe na daga cikin hamshakan da ke sha’awar sayen kungiyar.

Wasu rahotanni sun ce ana neman Fam biliyan 2.6 don sayar da Chelsea wadda a halin yanzu Abramovic ba shi da wani zabi da ya wuce ya sayar da ita bayan mallakarta kusan shekaru 20 da suka gabata.

A halin yanzu dai Abramovic na fatan gani ciniki ya fada kafin karshen wannan mako don gudun kada gwamnatin Birtaniya ta kara sanya masa wasu takunkuman da ka iya hana shi sayar da kuma ya tashi a tutar babu.

Abramovich ya amince zai shiga sulhu tsakanin Rasha da Ukraine

A bayan nan ne attajirin na Rasha ya ce ya amince da bukatar Ukraine na neman goyon bayansa wajen cimma matsaya kan yaki a Ukraine.

Mai magana da yawun mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ce yana kokarin taimakawa tun farkon da aka tuntube shi.

Ta ce wannan shigar ta hana Mista Abramovich- na hannun damar Shugaba Vladimir Putin fiye da shekaru ashirin- kan halin da ake ciki a Ukraine.

Wani babban dan kasuwar kasar Rasha- Oleg Deripaska – ya fitar da wata sanarwa da ke kira a kawo karshen jari-hujja a Rasha.

Hakan ya biyo bayan kalaman nasa a makon jiya, inda ya yi kira da a gaggauta tattaunawa kan zaman lafiya; yayin da wani attajirin Rasha, Mikhail Fridman, ya bukaci da a kawo karshen zubda jini.

FIFA da UEFA sun haramta wa Rasha doka wasanni

FIFA da UEFA sun sanar da dakatar da duk wasu kungiyoyin kwallon kafar Rasha gami da tawagar kwallon kafar kasar daga kowacce gasa saboda yakin da kasar ke yi yanzu haka da Ukraine.

Sanarwar da UEFA ta fitar ta ce kungiyoyin za su fice daga duk wata gasa da suke ciki har zuwa abin da hali zai yi.

Wannan mataki na UEFA nan una cewa tawagar kwallon kafar Rasha ta maza baza ta doka wasannin na suka rage mata na neman gurbi a gasar cin kofin duniya ba, haka zalika tawagar mata baza ta ci gaba da wasannin cin kofin euro ba.

Hukuncin na UEFA ya shafi hatta kungiyar Spartak Moscow wadda ke matakin kwata final a gasar Europa wanda zai taimakawa abokiyar karawarta RB Leipzig tsallake matsakin cikin sauki.

Bugu da kari EUFA ta dakatar da daukar nauyin kamfanin makamashi na Rasha Gazprom.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da FIFA da UEFA suka fitar, sun ce duniyar kwallo a hade take kuma suna tare da al’ummar Ukraine a wannan gaba.

Kafin tattaunawar kusoshin hukumomin biyu dai, a jiya FIFA ta sahalewa tawagar Rasha ta doka wasanninta amma ba tare da tuta ko taken kasa ba, amma wasu kasashen Turai suka yi tirjiya kan matakin.

Sai dai hukumar wasannin Rasha ta yi watsi da hukuncin hukumomin biyu tare da shan alwashin daukaka kara a kotun wasanni don neman adalci.