Jami’an tsaro sun rufe duk wasu hanyoyin shiga garin Dutsinma da ke Jihar Katsina, musamman hanyar Kankara zuwa Dutsinma da kuma hanyar Tsaskiya zuwa Dutsinmar.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, SP Gambo Isa ya fitar a wata takarda da aka raba wa manema labarai.
A cewarsa, rufe hanyoyin na da nasaba da batun kai ziyarar aiki da Shugaba Muhammadu Buhari zai yi a gobe Alhamis, 15 ga wannan wata.
Ana sa ran Shugaba Buhari zai ziyarci jihar ce domin bude sabon aikin da Gwamnatin Tarayya ta yi a Madatsar Ruwa ta Zobe.
Kazalika, akwai batun bude sabuwar hanyar da Gwamna Aminu Bello Masari ya gina wadda ta tashi daga garin na Dutsinma zuwa Tsaskiya ta dire har Karamar Hukumar Safana.
Har ila yau, sanarwar rufe hanyoyin ta gargadi masu ababen hawa musamman babura da makamantansu da su kiyaye wannan doka.
An shawarci masu yawace-yawacen da babu dalili da su takaita zirga-zirgasu ko kuma su bi wasu hanyoyin na daban maimakon manyan titunan da aka rufe.
Ana sa ran zuwan shugaban ya hada da hutun Babbar Sallah wanda ya saba zuwa gida Daura duk shekara.