✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina

Ɗaya daga cikinsu ya faɗi ya sume a lokacin da yake ƙoƙarin shiga rumfar da aka tanadar masu.

A wannan Litinin ɗin ce ne aka rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina waɗanda aka gudanar da zaɓensu a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025.

Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin.

Sai dai gab da lokacin da za a rantsar da su, ɗaya daga cikinsu ya faɗi ya sume a lokacin da yake ƙoƙarin shiga rumfar da aka tanadar masu.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori Honarabil Aminu Ɗan Hamidu shi ne wanda ya faɗi kuma aka ɗauka ranga-ranga zuwa asibiti.

Binciken da muka yi ya nuna cewa, shugaban ya take wani sashe na babbar rigar shi ne ba tare da ya yi la’akari ba yayin da ya yunƙura da ƙarfi don hawa matattakalar shiga rumfar, lamarin da ya janyo rigar ta shaƙe shi ya faɗi a sume.