✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe tashar lantarkin nukiliya daya rak a Iran

Iran ta rufe tashar wutar lantarkinta daya rak mai amfani da makamashin nukiliya.

Iran ta rufe tashar samar da wutar lantarkinta daga makamashin nukiliya guda daya rak da ta rage na wucin gadi saboda rashin kayan aiki.

Wani jami’in kamfanin lantarkin kasar, Gholamali Rakhshanimehr, ya ce rufe tashar nukiliyar da ke birnin Bushehr da aka yi ranar Asabar zai iya kaiwa kwana uku zuwa hudu kafin a sake budewa.

Gidan talabijin na kasar ya ruwaito shi yana cewa lamarin zai haddasa daukewar lantarki, amma bai yi karin haske ba.

Karon farko ke nan da Iran ta yi wa tashar da ke Kudancin kasar, rufewar gaggawa tun bayan bude ta a shekarar 2011 da taimakon kasar Rasha.

A karkashin yarjejeniyar hana Iran sarrafa nukiliya ta harkar soja, ana bukatar ta aika narkakken makamashin nukiliyar da ta sana’anta a tukwanen nukiliyarta zuwa Rasha.

A watan Maris, jami’in nukiliyar kasar, Mahmoud Jafari, ya ce akwai yiwuwar tashar ta tsaya da aiki saboda kasarsa ba ta iya samo kayayyakin da tashar ke bukata daga Rasha sakamakon takunkumin huldar banki da Amurka ta kakaba mata a 2018.

Tashar ta Bushehr na samun sinadarin uranium da take aiki da shi daga Rasha maimakon Iran.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Yaduwar Makaman Nukiliya (IAEA) ce ke sa ido a kan aikace-aikacen tashar, amma ta ki cewa uffan a kan rufe tashar.

Wani kwararre kan siyasar Gabas ta Tsakiya, ya fada wa kafar yada labarai ta Aljazeera cewa rufe tashar za ta fi yin tasiri a kan harkar samar da lantarki a Iran maimakon aikace-aikacenta na nukiliya.