✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rufe shagunan siyar da magani 434 a Jos

Mun ziyarci kantunan siyar magani manya da kanana guda 641 a Jos.

Majalisar Masana Kimiyyar Hada Magunguna ta Najeriya (PCN), ta sanar da rufe kantunan sayar da magani manya da kanana guda 434 a Jihar Filato.

Wannan dai na zuwa ne a sakamakon zarginsu da aikata laifuffuka daban-daban inda har aka damke wasu mutum biyu da suka yi wa majalisar kunnen uwar shegu.

Darakta a majalisar, Stephen Esumobi ne ya bayyana hakan a wajen taron manema labarai da suka kira ranar Juma’a a Jos, babban birnin jihar, bayan kammala aikin bincike na mako daya da suka gudanar a jihar.

Esumobi ya ce, tawagar majalisar ta kasance a jihar har na tsawon mako guda a kokarinta na wayar da kan masana ilimin hada magani da horar da su da kuma tabbatar da suna gudanar da harkokinsu kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce gabanin kammala ayyukan rangadin da suka yi, sun ziyarci kantunan siyar magani manya da kanana guda 641 a Jos.

Ya kara da cewa, daga cikin wannan adadi, an rufe shaguna 434 saboda aikata laifuffuka daban-daban, da suka hada da rashin lasisin, da rashin sabunta rijista, sayar da wasu magunguna da aka haramta da sauransu.

Kazalika, Esumobi ya ce sun damke wasu mutum biyu saboda sake bude shagunansu da suka bayan PCN ta rufe.