Gwamnatin jihar Oyo ta rufe wata masana’anta a garin Badun, bayan da aka tabbatar ma’akatan ta 30 sun kamu da cutar coronavirus.
Gwamnan jihar Seyi Makinde ne ya sanar da haka a shafin sa na Twitter a ranar Asabar, inda ya ce an samu karin majinyata 31 a jihar.
Mista Makinde ya ce sakamakon gwajin da aka yi wa mutum 31 ya tabatar da cewa suna dauke da cutar, lamarin da ya sanya adadin majinyata a jihar ya karu zuwa 107.
Ya kara da cewa “sabbin majinyata 30 ma’aikata ne a wata masana’anta a karamar hukumar Badun ta Kudu, kuma zuwa yanzu an rufe masana’antar.
“Ina kira ga al’ummar jihar Oyo da su kwantar da hankalinsu, kada kuma su tsorata, muna yin duk abin da ya dace domin magance lamarin, muna aikin nemo mutanen da suka yi hulda da majinyatan, za kuma mu shaida maku halin da ake ciki duk sanda muka dauki sabbin matakai”, inji Gwamna Makinde.
Ya ce ragowar mutum guda da ya kamu a baya-bayan nan daga karamar hukumar Ebgeda yake.
Jihar Oyo na cikin jihohin Kudu Maso Yamma da ba su dauki matakin kulle jama’ar su a gida ba, sai dai akwai dokar hana fitar dare da ta kafa domin hana yaduwar annobar a jihar.