Gwamnati ta bayar da umarnin rufe kafatanin makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da ke fadin Karamar Hukumar Wushishi a Jihar Neja.
Shugaban Karamar Hukumar Wushishi Danjuma Suleiman Nalango ne ya tabbatar da hakan a wata zantawa ta wayar tarho da ya yi da wakilinmu a ranar Lahadi.
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 8 a hanyar Bauchi
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 20 a kauyukan Kaduna
Nalango ya ce wannan dai na zuwa ne sakamakon tsammanin kai harin ’yan bindiga da ake yi a makarantun da zummar sace dalibai musamman a garin Zungeru da sauran makwatabta yankuna.
Ya ce bayanan sirri da hukumomin tsaro suka tattaro sun nuna cewa ’yan bindiga na shirye-shiryen kai hari da tsakar rana a wata Makatarantar Sakandire ta Mata da kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Neja da ke garin Zungeru.
A kan haka ne Nalango ya ce bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da suka hada da na Firamare, Sakandire da kuma na gaba da Sakandire da ke yankin.
A cewarsa, an dauki wannan mataki ne domin kaucewa makamancin abin da ya faru a garin Tegina, inda aka sace gomman dalibai a wata makarantar Islamiyyah.
Aminiya ta ruwaito cewa, ko a watan Maris na bana sai da Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun sakandire sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka yi kamari wajen sace dalibai.
A wancan lokaci dai Gwamnatin Jihar ta rufe makarantun sakandare 22 da suka hada ta na kwana 11 da na je-ka-ka-dawo 11, bayan sace dalibai a makarantar GSC Kagara, inda ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro a makarantu domin samar da ingataccen ilimi.