Jihar Zamfara ta rufe makarantunta a yankunan da ke iyaka da jihohin Katsina da Kaduna masu fama da matsalar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.
A sanarwar da ta fitar ranar Talata, Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce umarnin makarantu 10 ne aka rufe, a matsayin kandagarki, la’akari da yanayin tsaro.
- Yadda na kubuta daga hannun ’yan bindiga —Dalibin GSSS Kankara
- An gano inda daliban Makarantar Kankara suke —Masari
- Boko Haram ce ta yi garkuwa da daliban Kankara —Shekau
Kwamishinan Ilimin Jihar, Dokta Ibrahim Abdullahi Gusau, ya ce: “Abin da ya faru a makwabciyarmu jiyar Katsina ya tilasta mana rufe wadannan makarantu duk da cewa saura mako guda zangon karatun da ake ciki zai kare”.
Ya ce daukar matakin ya zama dole don a dakile rashin doka da oda a da kuma tabbatar da tsaron dalibai; duk da cewa za a ci gaba da sha’anin koyo da koyarwa a sauran makarantu.
“Makarantun da [umarnin] ya shafa na wurare ne da ke kan iyakar jiharmu da makwabtanmu, Katsina da Kaduna”, inji shi.
Makarantun da aka rufen su ne:
- G.S.S. Tsafe (Raka boarding)
- G.S.S Birnin Magaji (Boarding)
- G.D.S.S. Nasarawa Mailayi (je-ka, ka-dawo)
- G.D.S.S. Gusami (je-ka, ka-dawo)
- G.A.S.S. Zurmi (ta kwana)
- G.D.S.S. Gurbin Bore (Je-ka, ka dawo)
- G.G.S.S. Moriki (ta kwana)
- Science Secondary School, Shinkafi (ta kwana)
- Science Secondary School, Dansadau (ta kwana)
- Science Secondary School Bakkuyaum (ta kwana)