Za a sake rufe kasuwa bayan kwana 10 da budewa saboda saba ka’idojin hana yaduwar cutar COVID-19 a jihar Anambra.
Gwamnatin jihar za ta rufe kasuwar Awka daga ranar Litinin 15 ga watan da muke ciki saboda ‘yan tireda da sauran ‘yan kasuwa da dillalai sun karya sokar.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, C. Adinu ya fitar ranar Alhamis ta ce, “Sakamakon haka Gwamnatin Jihar Anambra za ta sake rufe Kasuwar Awka na tsawon mako biyu daga ranar 15 ga Yuni, 2020.
Da take sanar da bude kasuwanni bayan makonni biyar da rufe su domin hana yaduwar cutar, gwamnatin jihar ta shardanta wa amfani da kyallen rufe fuska da samar da kayan wanke hannu a kowane layi a kasuwanni.
- ‘Coronavirus ta kashe mutum 587 a Kano cikin mako biyar’
- Mutum 663 sun kamu da COVID-19 a rana guda a Najeriya
- COVID-19: Manyan jami’an gwamnati 8 sun kamu a Gombe
Haka kuma dole ne a rika wanke hannu akai-akai tare da bayar da tazarar taku shida tsakanin mutane.
Kwamishinan ya nuna damuwa kan yadda ya ce an yi watsi da matakan, musammanma a kasuwar ta Awka.