Gwamantin Jihar Neja ta ba da umarnin rufe daukacin makarantun sakandaren gwamnati da ke Jihar.
Kwamishinar Ilimin Jihar Hannatu Jibrin Salihu ta ce makarantun sakandaren za a rufe makarantun ne na tsawon mako biyu daga ranar Juam’a 12 ga watan Maris, 2021.
- Hare-haren Nasarawa da Zamfara sun lukume rayuka 30
- Ya kamata sojoji su bi Boko Haram har maboyarsu —Majalisa
Sanarwar da ta yi a safiyar Alhamis ta ce an dauki matakin ne bayan zaman da Ma’aikatar ta yi hukumomin tsaro.
Kwamishinar ta ce rufe makarantun gaba daya zai ba hukumomin tsaro isasshen lokacin yin cikakken nazari wanda bayan shi za su samar da ingantacce tsaro ga makarantun a fadin jihar.
Ta ce tun da farko Gwamnatin Jihar ta rufe makarantun sakandare 22 da suka hada ta na kwana 11 da na je-ka-ka-dawo 11, bayan sace dalibai a makarantar GSC Kagara.
Kwamishinar ta yaba wa iyayen dalibai da al’ummomi da suran masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi bisa hakuri da fahimtar da suka nuna.
Ta ce gwamnatin za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro a makarantu domin samar da ingataccen ilimi.
Ta kar da rokon jama’a su ci gaba da ba da goyon baya wajen samar da tsaro wanda matsalarsa ke barazana ga ilimi a jihar.