✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe banki saboda ma’aikacinsa na da coronavirus

An rufe babban reshen bankin First Bank, da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, bayan wani ma’aikacinsa ya kamu da cutar coronavirus a ranar…

An rufe babban reshen bankin First Bank, da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, bayan wani ma’aikacinsa ya kamu da cutar coronavirus a ranar Laraba.

Wata majiya ta tabbatar da cewa ana yi wa sauran ma’aikatan bankin gwajin cutar don gano ko akwai wadanda suka kamu da ita.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dokta Nimkong Lar ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa an samu wani ma’aikacin bankin First Bank, da ya kamu da cutar ta coronavirus a Jos.

Ya kuma ce an killace ma’aikacin ana yi masa magani, tare da kokarin gano wadanda ya yi mu’amula da su.

Sai dai ya ce hukumar gudanarwar bankin ce ta yanke shawarar rufe reshen bankin da kanta ba gwamnatin jihar ba.