kasar Bangaladesh ta zartar da hukuncin kisa a kan jagoran Jam’iyyar Musulunci mafi girma a kasar, Sheikh Moti’urr Rahman Nizami ta hanyar ratayewa, a babban gidan yari na Dhaka, babban birnin kasar.
Sheikh Moti’urr Rahman Nizami ya shafe shekara 15 yana shugabancin jam’iyyar ta Jama’at-e-Islami, inda ya kasance na hudu cikin jerin shugabanin Jam’iyyar Jama’at-e-Islami da aka aiwatar da hukuncin kisa a kansu a ‘yan shekarun da suka wuce.
An samu Mista Nizami, mai shekarA 73 da aikata laifuffukan cin zarafin dan Adam a lokacin yakin da Bangaladesh ta yi na neman ’yan cin kai daga kasar Pakistan a 1971.
A ranar Litinin Kotun koli ta Bangaladesh ta yi watsi da wani roko na karshe na a sake duba hukuncin kisan da aka yanke wa shaihin malamin. Kuma hakan ya sa aka rataye Nizami da misalin karfe 12:01 na daren shekaranjiya Laraba.
Hukumomin kasar sun tura karin ’yan sanda da masu tsaron kan iyaka zuwa birnin Dhaka da sauran manyan biranen kasar don tsaurara tsaro saboda Jama’at-e-Islami ta yi kiran yajin aiki na kasa a jiya Alhamis don nuna fushi da zartar da hukuncin.
Irin wannan hukunci da aka yanke a baya ya jawo tashin hankain da ya haddasa asarar rayukan mutum 200 galibinsu magoya bayan kungiyar da kuma ’yan sanda.
An rataye jagoran babbar Jam’iyyar Musulunci ta Bangaladesh
kasar Bangaladesh ta zartar da hukuncin kisa a kan jagoran Jam’iyyar Musulunci mafi girma a kasar, Sheikh Moti’urr Rahman Nizami ta hanyar ratayewa, a babban…