An rantsar da William Ruto a matsayin Shugaban Kasar Kenya na biyar bayan ya kayar da abokin hamayyarsa, Raila Odinga a zaben da aka gudanar a kasar a watan Agustan da ya wuce.
An dai gudanar da bikin rantsuwar ne a a filin wasa na Karasani da ke Nairobi, babban birnin kasar, kuma ya sami halartar shugabannin kasashen waje da dama, cikinsu har da Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo.
Babbar Jojin Kasar, Martha Koome, ce ta rantsar da shi a ranar Talata.
Mai shekara 55, William Ruto ya karbi rantsuwar ce da Kundin Tsarin Mulkin kasar a daidai lokacin da Kenya ke fama da fari da kuma tsadar rayuwa.
Da wannan rantsuwar dai, William shi ne na biyu daga kabilar Kalenjin da ya rike mukamin bayan marigayi Shugaba Daniel Arap Moi.
Sai dai babban abokin hamayyarsa, Raila Odinga ya kaurace wa bikin rantsuwar, inda ya ce nasarar da sabon shugaban ya samu a zaben cike take da alamomin tambaya.
William Ruto, wanda shi ne Mataimakain Shugaban da ya sauka, ya lashe zaben ne da kaso 50.5 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da shi kuma Raila Odinga ya sami kaso 48.8.
An dai ga cincirindon mutane suna ta shewa da daga tutocin kasar a filin rantsuwar, yayin da wasu kuma suke sanye da riguna masu launin ruwan kwai – wacce ita ce tutar yakin neman zabensa.