✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da sababbin shugabannin kungiyar ’yan kasuwa ta Jihar Filato

An gudanar da bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar ’yan kasuwa ta Jihar Filato a garin Jos, a ranar Asabar din da ta gabata.Wadanda aka…

Shugaba Mista Danjuma YerseAn gudanar da bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar ’yan kasuwa ta Jihar Filato a garin Jos, a ranar Asabar din da ta gabata.
Wadanda aka rantsar din sun hada da Mista danjuma Yerse a matsayin shugaba da Mista Mantim Lipdo, mataimakin shugaba na daya da Alhaji Yakubu Umar, mataimakin shugaba na biyu; da Alhaji Najib Abubakar shi ya zama sakatare da Misis Maurice D.Y. Mata da Eric Anlong, ma’ajiyi; da Moses Mafai, sakataren kudi; da Bwole Daugam, mai binciken kudi na daya da kuma Alhaji Sule Maidoki, mai binciken kudi na biyu.
Da take jawabi a wajen bikin, kwamishinar ciniki da masana’antu ta jihar, Misis Helen Maina ta bayyana cewa ma’aikatarta ta yi farin ciki da yadda ’yan kasuwar suka hada kansu suka zabi shugabannin a cikin kwanciyar hankali.
Ta ci gaba da cewa ma’aikatar na yin iyakar kokarinta wajen ganin harkokin kasuwanci suna tafiya kamar yadda ya kamata, musamman ganin yadda zaman lafiya ya dawo a jihar.
Daraktan harkokin kasuwanci a ma’aikatar, Mista Dauda Gashi, wanda ya wakilci kwamishinar, ya ce tana mika godiyarta ga ’yan kasuwar  kan irin goyan baya da hadin kan da suke baiwa gwamnatin jihar.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban karamar Hukumar kuan Pan, Honarabul Theoplius Dakassham ya ce ’yan kasuwa su ne kashin bayan cigaban tattalin arzikin kowace kasa a duniya.
Ya ce don haka karamar hukumarsa  take tafiya hannu da hannu da ’yan kasuwa don bunkasa harkokin kasuwanci a yankinsa da jihar da kuma kasa baki daya.
Sabon shugaban kungiyar, Mista danjuma Yerse kira ya yi ga gwamnatin jihar kan ta fito da wani shiri na musamman, don baiwa ’yan kasuwa bashin kudi domin su inganta kasuwancinsu.
Ya ce ’yan kasuwa masu son zaman lafiya ne, kuma a kullum suna ba da
gudunmawarsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, don haka akwai bukatar a tallafa musu.