A kasar Tanzaniya, an rantsar da Samia Saluhu ranar Juma’a a matsayin Shugabar Kasa, lamarin da ya mayar da ita mace ta farko da ta rike mukamin a kasar.
Hakan dai na zuwa ne bayan rasuwar Shugaba John Magufuli bayan ya sha fama da rashin lafiya.
- Kowa ya san Atiku ne ya lashe zaben 2019 — Gwamnan Bauchi
- ‘Shirin sauya tunanin tubabbun ‘yan Boko Haram ba ya aiki a Najeriya’
Mai kimanin shekaru 61 a duniya, Samia wacce musulma ce, ta fito ne daga yankin Zanzibar kuma za ta kammala wa’adin mulkin tsohon shugaban na shekaru biyar wanda zai kare a 2025.
Sanye da jan mayafi, an rantsar da ita a matsayin Shugabar Kasar ta shida a wani biki da ya gudana a birnin Darissalam kafin kuma daga bisani ta duba faretin da sojoji suka yi mata.
Hakan dai na nufin ita kadai ce za ta kasance Shugabar Kasa mace a nahiyar Afirka, in banda takwararta ta Habasha, Sahle-Work Zewde wacce ita ta jeka-na-yi-ka ce.
Mutane da dama dai a wajen kasar ta Tanzaniya ba su san sabuwar Shugabar ba har sai ranar Larabar da ta gabata inda ta bayyana a gidan talabijin domin sanar da rasuwar Magafuli.
Tsohon shugaban dai ya rasu ne yana da shekaru 61 a duniya bayan ya yi fama da ciwon zuciya wanda ya hana shi fitowa cikin mutane kusan tsawon makonni uku.