A ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, an sake rantsar da John Pombe Magufuli a matsayin Shugaban Kasar Tanzania a wani sabon wa’adi karo na biyu bayan lashe zaben kasar da aka gudanar a watan Oktoba.
Shugaba Magufuli da jam’iyyarsa ta Chama Cha Mapinduzi sun lashe zaben ne bayan samun kashi 84 cikin 100 na kuri’un da aka kada a yayin zaben wanda wasu rahotanni suka ce cike yake da rudani.
Alkalin Alkalan Tanzania, Mai Shari’a Ibrahim Juma ne ya rantsar da Magufuli a matsayin Shugaban Kasa da kuma Samia Suluhu Hassan a matsayin mataimakiyarsa.
Dubban al’umma sun halarci taron karbar rantsuwar da aka gudanar a filin wasanni na Jamhuri da ke Dadoma, babban birnin Kasar.
Haka kuma shugabanni da wakilai, da kungiyoyin duniya daga kasashe da daban-daban suka albarkaci taron karbar rantsuwar kama aiki.
Sabon wa’adin Shugaba Magufuli na tsawon shekaru biyar zai fara ne daga shekarar 2021 zuwa 2025 bayan ya faro wa’adinsa na farko daga 2015 zuwa 2020.
An ruwaito cewa Hukumar zaben Kasar Tanzania ta kare matakinta na sanar da sakamakon zaben wanda ya sha suka daga ’yan adawa da masu sanya ido.
A jawabinsa bayan karbar rantsuwa, Shugaba Magufuli ya sha alwashin yin aiki tare da dukkan al’ummar kasar ba tare da nuna banbancin addini, kabila, siyasa ko kalar fata ba domin ciyar da kasar gaba musamman a fannin tattalin arziki.