Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed a ranar Juma’a ya rantsar da Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a matsayin Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya.
Mohammed ya kalubalance ta da ta jajirce wajen ba marada kunya musamman ta hanyar tabbatar da kyakkyawar mu’amala da abokan aikinta.
Ya ce kasancewarta mace ta biyu da ta taba darewa kan kujerar, kamata ya yi ta tabbatar tana taruka akai-akai da sauran shugabannin kotunan da sauran alkalai don magance kalubalen da za su iya tunkarar su.
Babban mai shari’ar ya tunatar da ita cewar kasancewar kotun ita ce ta fi kowacce yawan alkalai, hakan ya nuna akwai namijin aiki a gabanta.
- Gwamnoni za su gana da Malami kan ‘yancin bangaren shari’a da na majalisa
- Kotun Daukaka Kara: Majalisa ta amince da Dongban-Mensem
- Buhari ya ayyana Dongban-Mensem Shugabar Kotun Daukaka Kara
“A iya sanina, Kotun Daukaka Kara ta fi kowacce yawan kararraki. Waje ne na aiki, waje ne da ke bukatar hadin kai. Amma ina da kwarin gwiwa cewa tarin iliminki zai taimaka miki wajen samun saukin aikin.
“Idan kika jajirce a kan abubuwan da na san ki da su, to hakika tarihi ba zai manta da ke ba”, inji Mohammed.
Da take mayar da jawabi, Mai Shari’a Dongban-Mensem ta ce sabon mukamin abin alfahari ne a gareta, ko da yake ta dauke shi a matsayin kalubale.
A cewarta, nadin nata ya biyo bayan shawarar da Hukumar Kula da Alkalai ta Kasa (NJC) ta bayar kuma shugaban kasa ya amince.
Ta ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa za ta yi iyakar kokarinta wajen ba marada kunya da kuma tabbatar da adalci.
“Zan yi kokari wajen dorawa kan kyawawan manufofin da magabatana suka aiwatar”, inji ta.