✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Daga yau, ƙasarmu za ta fara samun ci gaba kuma za a mutunta a duniya.

Donald Trump ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar Amurka na 47.

Trump ya karɓi rantsuwar kama aiki a sabon wa’adin mulki na shekaru 4 bayan nasarar da ya samu a zaɓen da ya gudana a watan Nuwamban da ya gabata.

A yayin jawabin da ya gabatar a Majalisar Tarayyar Amurka ta Capitol, Trump ya soki manufofi da tsare-tsaren gwamnatin da gabata musamman matakan da ta ɗauka a kan iyakokin ƙasar.

Ya ce gwamnati da ta gabata ta samar da mafaka ga “manyan masu aikata laifi” waɗanda suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

“Sabon babin ci gaban Amurka zai fara ne daga yau.

“Daga yau, ƙasarmu za ta fara samun ci gaba kuma za a mutunta a duniya.

“Zan sanya muradun Amurka a gaban komai,” inji Trump.

“Amurka za ta tanadi dakaru da ƙasashen duniya za su yi shakka ta yadda duk wani yaƙi da ake fafatawa a duniya zai zo ƙarshe.

“Sannan duk wani yaƙi da bai shafe mu ba ba za mu shiga ba saboda haka zan kasance jakadan zaman lafiya.”