✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rage kudin karatun Jami’o’i a Legas 

Gwamnatin jihar da sanar da zaftare kashi 65 cikin 100 na kudin makarantar da dalibai ke biya.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da rage kashi 65 cikin 100 na kudin karatu a jami’o’in jihar.

Tokunbo Wahab, mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin ilimi ne ya bayyana hakan da safiyar ranar Alhamis.

Wahab, ya ce gwamnatin za ta ci gaba da bayar da tallafi ga jami’o’inta tare da sanya su cikin yanayi mafi inganci a Najeriya.

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Legas (LASUSTECH) da Jami’ar Ilimi ta Jihar Legas (LASUED) na daga cikin wadanda za su amfana da wannan tagomashi.

Mahukuntan jami’o’in sun bayar da shawarar mayar da kudin makarantun zuwa Naira 195,000 kafin rage shi zuwa kashi 65% da Gwamna Sanwo-Olu ya sanar.

Shugaban Kungiyar Dalibai (SUG) ta Kwalejin Ilimi ta Adeniran Ogunsanya, Okeychukwu David, ya ce ya ji dadin wannan labari.

Gwamnan ya bayar da tabbacin duba yanayin rayuwa da ake ci don tallafa wa bangare ilimin jihar, don ganin dalibai sun samu ingantaccen ilimi da zai amfani al’ummar jihar da ma kasa baki daya.