✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nuna rashin gamsuwa da sakin Sheikh Abubakar

Shugaban Kasar Indoneshiya, Joko Widodo ya bayyana cewa ba za a saki mutumin da ake zargi da kitsa harin bam a garin Bali na kasar…

Shugaban Kasar Indoneshiya, Joko Widodo ya bayyana cewa ba za a saki mutumin da ake zargi da kitsa harin bam a garin Bali na kasar Indoneshiya, Sheikh Abubakar Bashir ba, har sai ya dauki alkawarin sassauta ra’ayinsa na tsaurin kishin addini.

Shugaban ya ce, malamin addinin dole ne ya amince kuma ya dauki alkawarin yin da’a ga dokokin kasa, muddin yana bukatar a sake shi daga tsaron da ake yi masa. Wannan bayani na Shugaban Kasar ya biyo bayan wata sanarwa ce da aka fitar a Jumu’ar da ta gabata, inda aka bayyana cewa za a saki malamin mai shekara 80 daga kaso saboda jinkai, saboda tsufa da rashin lafiyar da yake damunsa.

Sai dai kuma, tun bayan da aka sanar da wannan batu, aka yi ta samun korafe-korafe daga sassan duniya, inda suke bayyana cewa har yanzu hadari ne sakin malamin.

A shekarar 2002 ne dai aka kai harin bam din a garin Bali, inda mutum 202 suka rasa rayukansu, ciki kuwa har da mutum 88 ’yan kasar Australiya da  28 ’yan kasar Birtaniya.

Firayi Ministan Kasar Australiya, Scott Morrison ya shawarci Gwamnatin Indonesiya da ta tausaya wa mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon harin bam din. “Ba mu son mu ga an saki wannan mutum ya fito ya ci gaba da shirya kashe al’ummomin Australiya da na Indonesiya, domin kuwa babu abin da ya iya sai wa’azin nuna kiyayya,” inji shi.