✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manoma sun bukaci gwamnati ta biya diyyar takwarorinsu da aka kashe a Borno

Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN) ta bukaci gwamnati ta biya diyyar rayukan takwarorinsu kusan mutum 100 da aka kashe a jihar Borno a karshen makon…

Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN) ta bukaci gwamnati ta biya diyyar rayukan takwarorinsu kusan mutum 100 da aka kashe a jihar Borno a karshen makon da ya gabata.

Shugaban Kungiyar na kasa, Dokta Jones Ozuzu ne ya bayyana hakan a wurin wani taro da suka gudanar ranar Laraba a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Manoman sun aike da bukatar biyan diyyar ga iyalan abokan sana’arsu da aka kashe yayin wani harin da kungiyar Boko Haram ta kai a garin Zabarmeri na jihar Borno.

Dokta Jones ya kuma yi Allah-wadai da kalaman Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu kan kisan manoman kan samun izinin sojoji kafin zuwa gonakinsu.

A nasa jawabin, shugaban gamayyar Kungiyoyin Manoman Dawa ta Najeriya, Alhaji Lawal Gada, ya jajanta wa iyalan Manoman da aka yi wa kisan gilar.

Gada ya kuma yi kira ga gwamnati da ta yi tunani kan batun kiraye-kiraye da ake mata kan yunkurin sake bude iyakokin kasar nan.