Ministan Ma’aikatar Kimiyya Da kere-kere, Dokta Ogbonnaya Onu ya yi kira ga Cibiyar Hannun Jari da ta duba yiwuwar sake saka wasu kamfanonin sadarwa cikin kasuwar hannun jari da nufin inganta tattalin arzikin kasa ta hanyar bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu.
Da yake jawabi a wajen gabatar da cibiyar bayanan kasuwar hannun jari, wacce aka kashe Naira miliyan 500 wajen samar da ita a Legas kwanakin baya, Dokta Onu ya bayyana cewa bai kamata Najeriya ta rike hannunta tana tokabo da cewa ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Afrika ba kawai, ya zama wajibi ta kara azama domin wuce wannan matsayi nata a yau.
Ministan ya yaba wa Cibiyar Hannun Jari ta Najeriya, saboda yadda take taimaka wa kasa wajen bunkasa tattalin arziki. “Na lura da cewa Kasuwar Hannun Jari tana da babban buri fiye da yadda kowa ke tsammani. Ina da yakinin cewa za ku iya zama mafi girma a duniya, nan ba da jimawa ba,” a cewarsa.
Dokta Onu ya ce Ma’aikatar Al’amuran Kimiyya Da kere-kere tana kan hanyar fito da shirye-shirye da za su ba kasar nan damar zama mai dogaro da kanta.
Tun da farko, Babban Shugaban Kasuwar Hannun Jari, Mista Oscar Onyema, OON ya bayyana cewa wannan cibiya ta bayanai tana kunshe da ingantattun na’urori domin gudanar da ayyukanta da suka danganci hannun jari cikin sauki da gamsarwa.
Kamar yadda Mista Onyema ya bayyana: “Cibiyar Bayanai za ta rika gamsar da ’yan kasuwa da ma dukkan wani mai bukata a cikin farashi mai rahusa kuma cikin matukar gamsarwa. Za ta iya biyan bukatar abokin huldar da ke zaune nesa da cibiyar da kilomita 25.”
Ita dai Cibiyar Kasuwancin Hannun Jari ta Najeriya tana daya daga cikin manyan cibiyoyin tattalin arziki mafi girma a Afrika kuma ita ce giwa ja-ga wajen bunkasa tattalin arzikin Afrika.