Rahotanni daga birnin Dikko sun ce an nada tsohon dan Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mohammed Ida a matsayin Wazirin Katsina.
Sarkin Yakin Katsina kuma Sakataren masarautar, Alhaji Bello Mamman Ifo ne ya tabbatar wa BBC ranar Talata.
- Kayayyaki sun tashi a Najeriya saboda tsadar farashin mai —NBS
- Dan shekara uku ya kashe mahaifiyarsa bisa kuskure
Sanata Ida ya maye gurbin Alhaji Sani Abubakar Lugga wanda ya yi murabus daga mukamin nasa na Wazirin Katsina a watan jiya.
Sanata Ida shi ne yake rike da sarautar Sardaunan Katsina kafin nadin nasa.
An haifi Sanata Ida a birnin Katsina a shekarar 1949, kuma ya yi karatunsa na boko a Najeriya da Birataniya da kuma Amurka.
Sabon Wazirin na Katsina ya soma aikin gwamnati da Babban Bankin Najeriya, kuma ya rike mukamai da dama a gwamnati, ciki har da Babban Sakatare na Ma’aikatar Tsaron Najeriya.
Sannan ya wakilci shiyyar Katsina ta Tsakiya a Majalisar Dattawan kasar tsakanin 2007 zuwa 2011.
Sanata Ida yana da mata daya Hajiya Khadija da ‘ya’ya da jikoki da dama.