✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An nada Mukaddashin Shugaban Hukumar NECO

Hakan na zuwa ne bayan kwana hudu da mutuwar Shugaban Hukumar.

Majalisar Gudanarwa ta Hukumar Shirya Jarrabawa a Najeriya NECO, ta amince da nadin Mista Ebikibina John Ogborodi a matsayin Mukaddashin Shugaban hukumar.

Hakan na zuwa ne bayan kwana hudu da mutuwar Shugaban Hukumar, Farfesa Godswill Obioma kamar yadda Kakakinta, Mista Azeez ya sanar.

Kafin nadin nasa, Mista Ogborodi shi ne Daraktan Ayyuka na Musamman a Hukumar.

Mista Ogborodi wanda dan asalin Karamar Hukumar Sagbama ta Jihar Bayelsa ce, ya fara aiki da NECO a 1999 inda ya rike mukamai daban daban.

Ya yi Digiri na farko a Jami’ar Jos a shekarar 1986 sai kuma na biyu a wannan jami’a a shekarar 1999.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Litinin da ta gabata ce Farfesa Godswill Obioma ya koma ga Mahaliccinsa bayan ya sha fama da gajeriyar jinya.