✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Farfesa Bashar Aliero Shugaban Jami’ar Jihar Kebbi

  Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Aliero a qarqashin shugabancin Manjo Janar Muhammadu Magoro (mai ritaya) ta amince…

 

Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Aliero a qarqashin shugabancin Manjo Janar Muhammadu Magoro (mai ritaya) ta amince da nadin Farfesa Bashar Ladan Aliero a matsayin sabon Shugaban Jami’ar.

Wannan bayani ya fito ne a wata sanarwa da Kakakin Jami’ar, Malam Husaini Adamu Zuru ya sanya wa  hannu kuma aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi.

Sabon Shugaban Jami’ar, malami ne a Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato, kafin nada shi.

Kakakin Jami’ar ya shaida wa manema labarai cewa: “Shugaban Majalisar Gudanawar Jami’ar, Manjo Janar Muhammadu Magoro (mai ritaya) da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu sun amince da nadin Farfesa Bashar Ladan Aliero a matsayin sabon shugaban jami’ar.”

Ya qara da cewa: “Tuni Farfesa Bashar Aliero ya karbi ragamar tafiyar da Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Aliero daga hannu Farfesa Bello Shehu Malami wanda ya shugabanci jami’ar na tsawon shekara biyu.”

Daga nan ya ce, Gwamna Bagudu da Janar Magoro da dukan ma’aikatan jami’ar sun yi wa sabon shugaban fatan alheri da kuma murnar zama shugaban jami’ar.