Gwamnatin Jihar Gombe ta nada Alhaji Ahmed Mohammed Usman a matsayin sabon Sarin Deba. Sabon Sarkin ya gaji marigayi Sarkin Deba Laftana Kanar Abubakar Waziri Mahdi, Sarki na 36 wanda ya rasu a ranar Alhamis 23 ga Maris din bana. Kwamishinan Kasanan Hukumomi da Harkkokin Masarautu na Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Abubakar Walama ne ya mika wa sabon Sarkin takardar nada shi a sarautar a ranar Talatar da ta gabata, inda ya zama Sarkin Deba na 37 kuma Sarkin yanka na 2 a masarautar.
Kafin nada Alhaji Ahmed Mohammed Usman, shi ne Daraktan Sashin Kula da bin Ka’idoji a Gwamnatin Jihar Gombe.
An haifin sabon Sarkin ne a ranar 23 ga Oktoban a 1963 a garin Deba kuma ya yi karatu a F iramaren Central ta Deba a 1970 zuwa 1976 daga nan ya tafi Sakandaren Gwamnati ta Bauchi a 1976 zuwa 1981 bayan ya gama sai ya wuce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a tsakanin ta 1982 zuwa 1986 inda ya samu Digiri a ilimin safiyo.
Alhaji Ahmed Mohammed Usman, ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban sashin kula da sanin darajar kadarori da ke Abuja sannan ya zama mataimakin darakta a Hukumar Bunkasa Yankunan kan Iyaka (Boarder Communities Debelopment Agency) a shekara ta 2010 zuwa 2011, daga nan sai ya zama babban mai taimaka wa Gwaman Jihar Gombe a bangaren kula da bin ka’idoji waen bayar da kwangilolin gwamanti wato Due Process.
Ya zaman Darakta a wannan sashi a shekara ta 2015 zuwa yanzu da aka nada shi ya sabon Sarkin Deba mai daraja ta 1a ranar Talata 8 ga watan Agusta.
Shi dai marigayi Sarki Laftana Kanar Abubakar Waziri Mahdi, ya karbi sarauta ce a 1984 inda ya gaji kakansa. Marigayin tsohon soja ne da ya kai mukamin Laftana Kanar kafin ya zama Sarki.