✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An mika wa Masu Zaben Sarkin Zazzau takardar tuhuma

Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar Kaduna ta ba Masu Zaben Sarki hudu daga cikin biyar takardar tuhuma (Query) kan rashin halartar taron shirye-shiryen…

Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar Kaduna ta ba Masu Zaben Sarki hudu daga cikin biyar takardar tuhuma (Query) kan rashin halartar taron shirye-shiryen bikin mika sandar sarauta da kwamishinan ya kira a ofishinsa.

Takardar da aka mika musu a ranar 13 ga Nuwamba, 2020 mai lamba MLGCA/36/VOL: Vi/1059 tana dauke ne da sanya hannun Babban
Sakataren Ma’aikatar, Musa Adamu.

Wanda aka mika wa takardar sun hada da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu; Makama Karami, Alhaji Mahmoud Abbas; Limamin Juma’a, Sheikh Dalhatu Kasimu da kuma Limamin Kona Imam
Sani Aliyu.

A cikin takardar ana tuhumarsu kan rashin halarta zaman da aka  gayyace su a ofishin kwamishinan don tsare-tsaren mika sandar sarauta ga sabon Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ranar 30 Oktoba 2020.

Takardar ta bukaci Masu Zaben Sarkin su ba da ama cikin awa 48 ko gwamnati ta dauki matakin ladabtarwa a kansu.

Sai dai masu sharhi suna zargin cewa yin hakan zai kara haifar da matsala ce ba gyara ba, saboda a lokacin da aka gayyace su maganar na
gaban kotu.

Wata majiya a masarauta ta ce a halin yanzu dai ba a ji daga bangaren gidan Fagacin Zazzau ba, saboda haka ba za a iya tantancewa ko an ba shi takardar tuhumar kamar yadda aka ba sauran mutane hudun ba.

Aminiya ta yi kokarin tuntubar daya daga cikin wadanda aka ba akardar, ko Masarautar Zazzau don jin ta bakinta amma hakarta bai cimma ruwa ba don ba wanda ya yarda ya ce uffan game da batun.