✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An masa ɗaurin rai da rai saboda lalata almajirai 2 a Sakkwato

Alƙalin kotun ya ce laifin ya saɓa da ɗabi'ar ɗan Adam.

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Jihar Sakkwato, ta yanke wa wani mutum mai suna Sani Ibrahim hukuncin ɗaurin rai da rai saboda yin lalata almajirai guda biyu.

Kotun ta soke hukuncin wata kotu ta yi masa na ɗaurin shekara uku, bisa laifin yi wa almajiran ƙarfa-ƙarfa.

Mai shari’a Ebiowei Tobi, wanda ya yanke hukuncin, ya ce kotun farko ta yi kuskure wajen ƙin amincewa da shaidun waɗanda abin ya shafa.

Kazalika, rahoton asibiti na ɗaya daga cikin waɗanda aka lalata ya tabbatar da aikata laifin.

Mai shari’a Tobi ya bayyana cewa wannan laifin abin kunya ne kuma ya saɓa wa ɗabi’ar ɗan Adam.

Don haka, ya maye gurbin hukuncin kotun farko da hukuncin ɗaurin rai da rai.

Bayan yanke hukuncin, babban lauyan jihar, Barista Murtala Gidanmadi, ya yaba da hukuncin.

Ya bayyana cewa hakan zai zama izina ga masu aikata irin waɗannan laifuka.