✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An masa ɗaurin wata 2 kan satar kayan marmari

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Mayu.

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari a Jihar Kaduna, ta yanke wa Zahradeen Garba mai shekara 32 hukuncin ɗaurin wata biyu a gidan gyaran hali, bisa samunsa da laifin satar kayan marmari.

Alƙalin kotun, Anas Khalifa, ya yanke hukuncin ne bayan Garba ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa.

Sai dai Khalifa ya ba shi zaɓin biyan tarar Naira 10,000, ko kuma ya biya wanda ya shigar da ƙara, Abba Zakari Naira 77,000.

Tun da farko, mai gabatar da ƙara, ASP Luka Sadau, ya ce mai kayan ya shigar da ƙara ne a ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari cewa wanda ake tuhuma da wani Bashir Aminu ne suka aikata laifin.

“Ku biyu kun haɗa baki kuka ƙwace baron mai ƙara wanda ke ɗauke da dabino, kwakwa da tsabar kudi Naira 66,850.

“A lokacin gudanar da bincike, kun amsa laifin aikata satar kayan kuma kun sayar wa wani Sulaiman a kan Naira 15,000,” in ji Sadau.

Wanda ake tuhuma, Aminu, ya musanta aikata laifin.

Alƙalin kotun ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Mayu domin bai wa mai gabatar da ƙara damar gabatar da shaidu.