✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An maka sarakuna a kotu kan sayar da gonar wani

Ana tuhumar sarakunan da hada baki wajen aikata babban laifi.

Wasu sarakunan gargajiya uku sun gurfana a gaban kotu kan zargin sayar da wata gona ba tare da sanin mai ita ba.

A ranar Talata aka gurfanar da sarakunan tare da wasu mutum uku a gaban kotu a Makurdi, babban birin Jihar Binuwai, bayan mai gonar ta kai kara cajis ofis cewa ta ga wasu a cikin gonarta suna sare mata bishiyoyi ba tsare da saninta ba.

’Yar sanda mai gabatar da kara, Veronica Shaagee, ta shaida wa kotu cewa, mai gonar ce ta kai kara cajis ofis ne cewa ta ga wasu a cikin gonarta suna sare mata bishiyoyi ba tsare da saninta ba.

Ta kara da cewa ko da mai gonar ta tambayi mutanen daga ina? Kuma wa ya ba su izinin sare mata bishiyoyi, sai suka ce sayen gonar suka yi.

Bayan gudanar da bincike kan batun ’yan sanda suka kama wasu sarakunan yankin tare da wasu mutum uku kan badakalar sayar da gonar.

Mai gabatar da karar ta ce, ana tuhumar wadanda ake zargin ne da hada baki wajen aikata babban laifi, wanda ya saba wa sassa na 97 da 349 da 329 na Kundin Dokokin Jihar Binuwai na 2004.

Alkalin kotun, Mista Vershima Hwande, ya bayar da belin sarakunan saboda matsayinsu, sauran kuma a kan kudi  N100,000 kowannensu.

Mai Shari’a Hwande ya dage shari’ar zuwa ranar 1 ga Fabrairu, 2023.