An maka wani kwamishinan tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a kotu kan zargin aibata auren zawarawa da gwamnatin jihar mai ci ta aiwatar kwanan nan.
Wasu daga cikin wadanda suka ribatu da auren zawarawan da aka gudanar makonni kadan da suka gabata ne suka yi karar tsohon Kwamishinan Ruwa na jihar, Alhaji Garba Yusuf Abubakar kan zargin aibata aurensu da ya yi.
- Ana zargin mai shekaru 55 da yi wa karamar yarinya fyade a Gombe
- ‘Ya kamata matasa su jagoranci gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya’
Tuni dai Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kasuwa mai zamanta a Unguwar Shahuci ta sanya ranar 6 ga watan Nuwamba, 2023 don fara sauraren karar da ma’auratan suka shigar.
Masu karar sun zargi tsohon Kwamishinan da yin kalaman batanci ga auren nasu a kafafen watsa labarai, lamarin da ya sa suka garzaya gaban kotun don neman ta bi musu hakki.
Wani daga cikin masu karar ya bayyana cewa, “A gaskiya kalaman da tsohon Kwamishinan ya yi sun tayar mana da hankali domin mun ji yana fadin cewa wai auren bai dauru ba.
“Kuma ko an haifi yara to a cewarsa ’ya’yan gaba da alfatiha ne da sauransu.
Ita ma wata mata ta bayyana cewa sun ji yadda Kwamishinan yake aibata aurensu don haka suka nemi kotun ta gurfanar da wadanda ake zargi gabanta.”
Kan haka ne Alkalin Kotun Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya ya ce ya sanya 6 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a soma sauraron shari’ar.