Wasu tsofafin daliget din jam’iyyar APC sun maka ta a gaban kotu kan kokarin musanya sunan Kabiru Ibrahim Masari daga matsayin Mataimakin dan takarar jam’iyyar na Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.
Tinubu ya dauki Masari ne a matsayi mataimakinsa na wucin gadi kafin shi da jam’iyyar su fitar da sunan mataimaki na din-din-din kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shardanta, gudun karewar wa’adi.
- Munanan hare-hare 12 da aka taba kai wa gidajen yari a Najeriya
- Sallah: Gwamnatin Najeriya ta ayyana hutun kwana biyu
Zakari Maigari da Zubainatu, jiga-jigan guda biyu da suka shigar da karar dai daliget ne a zaben da aka yi na fid-da gwani na jam’iyyar wanda aka yi a Abuja.
Mutanen biyu sun kuma shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya ne su na bukatar ta hana APC cire sunan Masari daga matsayin Mataimakin na Tinubu kamar yadda jam’iyyar ta ke shirin yi.
Suna mai cewa a karar ta su, “Janye sunan Masari na zama tamkar haramta takarar jam’iyyar ce baki dayanta a zaben mai zuwa”.
Masu karar sun kuma yi nuni da sashe na 142 (1); 29 (1) 33 da kuma 33 na dokar zabe a matsayin madogara.
Sannan suna takaddamar cewa sassan sun haramta janyewar Masari a matsayin Mataimakin Tinubu a zaben Shugaban Kasa a jama’iyyar APC da har za a iya cire ko a musanya shi da wani.
Kotun dai ba ta sa ranar fara sauraron shari’ar ba tukunna.