An gurfanar da Alkalin wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Tudun Wadan Zariya a gaban wata Kotun Majistire kan zargin bayar da umarnin rusa gidan wasu magada da aka mutu aka bari.
Ana dai tuhumar Malam Ibrahim Inuwa a matsayinsa na babban jami’in gwamnati da aikata ba daidai ba wanda ya saba wa sashe na 58 da 89 da kuma 312 na dokokin finar kod na Jihar Kaduna.
- Yadda tattalin arzikin Nijeriya ya tabarbare a cikin shekara 10 da suka gabata
- An tarwatsa masu zanga-zanga da barkonon tsohuwa a Gonin Gora
Wani lauya mai suna Abdullahi Y Ladan ne ya shigar da kara a madadin Rabi Abdullahi da ’ya’yanta da ake zargi alkalin ya bayar da umarnin a rusa gidan da suka gada a wajen mijinta marigayi.
Bayanai sun ce Malama Rabi wadda ke cikin takaba bayan rasuwar mijinta kwanaki 14 tana zaune kawai sai ta ji ana rusa gidan babu wata sanarwa, inda a halin yanzu ita da ’ya’yanta suka rasa matsugunni.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, tun farko dai Malama Rabi ba ta cikin ƙunshin waɗanda wata mata mai suna Hajiya Sa’adatu Muhammed wadda tsohuwar matar yayan mijinta, ta kai ƙarar marigayin duk da cewa ba ta da gadon mijinta saboda shekaru 23 ke nan da mutuwar aurensu.
A cewar Hajiya Rabi yayin zantawa da Aminiya, “yanzu haka ba mu da inda za mu zauna da ’ya’yana domin na samu na ci gaba da takaba, sai da wani surukina ya ɗauke ni ya maida ni gidan shi.
“Sa’adatu ce ta kai karar neman gadon tsohon mijinta duk da cewa ba ta da hurumin cin gadonsa sakamakon shekaru 23 ke nan da rabuwar auren nasu da ita sannan kuma bayan na ya kara wani aure.
“Amma duk da haka sai Alkali Ibrahim Inuwa ya ba da umurnin a rusa gidan a maimakon ci gaba da shari’ar takaddamar rabon da ke gaban shi wadda ya kamata a dawo domin ci gaba da sauraron ƙara a ranar 21 ga watan Fabarairu 2024,” inji Malama Rabi.
A cewarta wannan rashin bin doka da Alƙali Ibrahim Inuwa ya yi ya haifar da tsoro da firgici ga mazauna yankin saboda hatta mai unguwar yankin ba a sanar da shi ba.
Shi kuwa lauya mai shigar da kara, ya ce ita kuma wadda yake kara ta biyu — Hajiya Sa’adatu Muhammed — ta aikata ba daidai ba saboda ta cimma wata manufa da ke tsakaninta da marigayin wanda yayan tsohon mijinta ne duk da cewa ya rasu.
Lauyan ya nemi Kotun da ta tabbatar da adalci kan alƙalin da ake tuhuma muddin an same shi da laifi kamar yadda doka ta tanada sannan ta ɗora masa alhakin sake gina gidan da aka rusa da kuma biyan diyyar kuɗi Naira miliyan biyar saboda asarar kayayyaki da firgita mazaunan gidan.
Da take yi wa Aminiya bayani, Malama Rabi Abdullahi ta ce da wata safiya ce suna zaune a ɗaki sai kawai suka ji ana sarar ginin gidan wasu kuma daga sama na yaye rufin kwanon gidan.
A cewarta ko da suka fito waje domin ganin abin da ke faruwa sai suka ga jami’an tsaron Sibil Difens ɗauke da bindigogi sun tare duk wata hanyar zuwa gidan domin cika umarnin kotu.
Wannan lamari dai ya tayar wa mazauna unguwar hankali waɗanda suka riƙa jajanta wa mazauna gidan da abin ya shafa.
Aminiya ta tuntubi wakilin Masarautar Zazzau da ke unguwar, Alhaji Garba Ibrahim Marafa wanda shi ne dagacin gundumar Tukur-Tukur domin jin ta bakinsa, inda ya ce,” kasan sha’anin kuto babu wanda ya sanar da ni duk da ina makwabtaka da gidan.
Ya kara da cewa a lokacin ya je wurin jami’an tsaron Sibil Difens sun kewaye ko’ina.
“Ni abin da na sani shi ne tun lokacin da mijin ita Rabi na raye ake ta turka-turka kan maganar gidan.
Aminiya ta ziyarci ofishin jami’an na Sibil Difens domin jin ta bakinsu, inda suka gabatar da shaidar takardar da Kotu ta rubuto na neman kariyarsu domin gudanar da wannan aiki.
Kazalika, Aminiya ta garzaya Kotun domin neman takardar hukuncin shari’ar da ya sanya ɗaukar wannan mataki na rushe gidan magada a maimakon rabon gado idan akwai takaddama.
Sai dai hakar Aminiya ba ta cimma ruwa ba saboda Kotun ta buƙaci wakilinmu da ya rubuto takardar buƙata kafin su ba shi duk da cewa akwai dokar neman bayanai da ta bai wa manema Labarai damar samun bayanai ba tare da wata takarda ba.