Rahotanni daga Faransa sun ce akalla kaburbura sama da 100 na Yahudawa ne aka lalata a kusa da Strasbourg da ke gabashin kasar, a wani yunkuri na nuna wariya a gare su.
Shugaban Kungiyar Yahudawa da ke Faransa, Maurice Dahan ya bayyana kaduwa da matakin, inda ya bukaci hukumomi su dauki mataki a kai.
Shugaba Emmanuel Macron da ya ziyarci wurin domin gani da idonsa, ya sha alwashin magance matsalar kalaman batanci da kuma fadakar da daliban makarantu muhimmancin watsi da shi.
Gwamnatin Faransa ta sanar da daukar matakan hukunta masu aikata irin wadannan ayyuka da ke tayar da hankulan jama’a.