Tsohon Kwamishinan Ayyyuka na Jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya, ya caccaki gwamnatin Jihar Kano kan gaza biyan albashin ma’aikatan jihar duk da zuwan bikin sallah karama.
Dan Sarauniya ya yi caccakar ce a shafinsa na Facebook, inda ya zargi gwamnatin jihar da kwasar dukiyar al’umma wajen biya wa wasu shafaffu da mai kudin zuwa aikin Umrah.
- FiFA ta ci tarar Senegal kan haske Salah da fitila
- Yadda aka gudanar Hawan Sallah a masarautar Zazzau
“Anje Umra da dukiyar baitilmali an dawo, har yau hakkin ma’aikata kuma ba a basu ba..Sallah guda…to me ne amfanin Umarar?.
Tuni dai ma’aikatan jihar tun kafin gudanar da bikin sallar a ranar Litinin, suka shiga kokawa kan yadda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi burus da su, duk da irin tarin tsarabe-tsarabe da sallah ke zuwa da shi.
Hakan ya sanya ma’aikatan jihar da dama yin sallah lami, wasu da dama ma ko abincin sallah ba su damar yi ba.
Wasu kuma sun gudanar da sallar saisa-saisa, wato babu yabo babu fallasa.
Dan Sarauniya dai ya yi kaurin suna wajen caccakar gwamnatin Ganduje tun bayan dan gwamnan ya tunbuke shi daga mukaminsa na Kwamishina.
Ko a baya-bayan nan, sai da gwamnatin Jihar ta maka shi a kotu kan zargin cin zarafin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, lamarin da ya sanya shi zuwa gidan dan-kande kafin daga bisani ya samu beli.
Sai dai tsohon Kwamishinan bai daina wallafa ire-iren kalaman da kotu ta hane shi da yin su ba.