✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwashe sama da tirela 400 ta shara cikin kwana 3 a Kano

Gwamnan Jihar ya jadadda aniyar tsaftace jihar daga kazanta.

Kwamitin Tsaftace Muhalli a Kano, ya kwashe sama da tirela 400 ta shara a sassan birnin jihar cikin kwana uku.

Aliyu Yakubu Garo, Babban Sakatare a Ma’aikatar Muhalli ta jihar, ya tabbatar da kwashe sharar a yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai ranar Alhamis.

Bayanai sun ce Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya kafa kwamitin hadin gwiwa kan aikin kwashe sharar da aka soma a wannan makon.

Aikin na da nufin tabbatar da yashe magudanan ruwa da ke haifar da ambaliya a lokacin damina.

Haka kuma, ana kokarin tabbatar da kawar da shara ta yadda za a tsaftace tituna a jihar.

Babban sakataren, ya ziyarci wurare kusan 20 da ake gudanar da aikin, ya kuma yaba wa jama’a bisa hadin kai da goyon baya wajen ganin an samu nasarar kwashe sharar.

Garo ya yaba wa shugaban kwamitin, Ahmadu Danzago da sauran masu ruwa da tsaki bisa jajircewa da hadin kai da suka bayar wajen ganin an gudanar da aikin cikin nagarta.

Ya kuma bukaci mazauna jihar da su mayar da hankali wajen share magudanun ruwa a kai a kai domin guje wa hadarin ambaliyar ruwa.

Ya ce gwamnatin Abba a cikin kankanin lokaci ta nuna sha’awar kare rayuka ta hanyar inganta tsaftar muhalli.

An kuma umarci mazauna jihar da su ke yin amfani da kwandon shara, domin tsaftace jihar daga kazanta.

Ya bukaci mazauna jihar da su kara kaimi ga kokarin gwamnati na kare muhalli daga illolin sauyin yanayi.

Garo ya ce idan aka ci gaba da aikin kwashe sharar a Kano, birnin zai samu yanayi mai kyau.