✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LABARIN RFI: Messi ya yi awon gaba da magoya bayan PSG

Adadin magoya bayan PSG a shafinta na Instagram ya ragu sosai tun bayan da aka sanar cewa, Lionel Messi zai raba gari da kungiyar

Adadin magoya bayan PSG a shafinta na Instagram ya ragu sosai tun bayan da aka sanar cewa, Lionel Messi zai raba gari da kungiyar.

A bangare guda kuma, adadin magoya bayan Inter Miami ya karu a Instagram sakamakon shirye-shiryen kulla yarjejeniya da dan wasan.

Yanzu haka Inter Miami ta Amurka ta samu karin sama da magoya baya miliyan 3 a shafin nata, inda kuma PSG ta Faransa ta yi asarar magoya baya sama da miliyan 2 a cikin kwanaki bakwai da suka gabata kadai.

Adadin magoya bayan PSG a Instagram din ya koma miliyan 67.8 daga miliyan 69.9.

Ita kuma Miami, adadin magoya bayanta yanzu ya kai miliyan 4.8 daga miliya 1 kacal.

Messi kadai na da magoya baya miliyan 469 a shafinsa na Instagram.