✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwana ana barin wuta a garin Kalaba

An kwana ana harbe-harbe da kona gidaje a unguwannin O’Oba da Itega Okpame na Karamar Hukumar Yala ta Jihar Kuros Riba. Ba a kai ga…

An kwana ana harbe-harbe da kona gidaje a unguwannin O’Oba da Itega Okpame na Karamar Hukumar Yala ta Jihar Kuros Riba.

Ba a kai ga tantance girmar barnar da aka yi ba, amma wasu majiyoyinmu sun tabbatar da mutuwar mutum biyar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Alhassan Aminu ya tabbtar da faruwar lamarin inda ya ce an tura ’yan sanda domin tabbatar doka da oda a yankunan.

“Zauna-gari-banza ne daga O’Oba suka mamaye wasu unguwanni suna harbe-harbe. Ina sane na kuma tura jami’anmu zuwa wuraren…”